Noble Quran » Hausa » Sorah An-Naba' ( The Great News )
Choose the reader
Hausa
Sorah An-Naba' ( The Great News ) - Verses Number 40
وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا ( 12 )  
 
Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
وَأَنزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاءً ثَجَّاجًا ( 14 )  
 
Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًا ( 17 )  
 
Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا ( 18 )  
 
Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.
وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا ( 20 )  
 
Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا ( 24 )  
 
Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًا ( 27 )  
 
Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
فَذُوقُوا فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا ( 30 )  
 
Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًا ( 35 )  
 
Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
رَّبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرَّحْمَٰنِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا ( 37 )  
 
Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا ۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَٰنُ وَقَالَ صَوَابًا ( 38 )  
 
Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
ذَٰلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ مَآبًا ( 39 )  
 
Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًا ( 40 )  
 
Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"
Random Books
- TUSHE UKU NA MUSULUNCI-Formation : محمد بن عبد الوهاب Source : http://www.islamhouse.com/p/589 
- SU WANE NE MASOYAN AHLUL BAITI ?SU WANE NE MASOYAN AHLUL BAITI ?Source : http://www.islamhouse.com/p/156352 
- TAFSIRIN USHURIN KARSHE NA AL KURANI MAI GIRMA-Source : http://www.islamhouse.com/p/250950 
- ALKUR'ANI MAI GIRMA Da Kuma Tarjaman Ma'anõninsa Zuwa Ga Harshen HAUSA-Reveiwers : Malam Inuwa Diko Translators : Abubakar Mahmud Gummi From issues : Wuri Da Aka Tanada Musamman Don Buga AlRur'ani Mai Girma Na Mai Kula Da Masallatai Biyu Masu Tsarki Sarki Fahad Source : http://www.islamhouse.com/p/597 
- KYAKKYAWAR SAFIYA-Source : http://www.islamhouse.com/p/156350 















